Me ya rage wa Amurka da Ukraine bayan raba gari?

Tun daga isa fadar White House Mr. Zelenskyy ya fara shan caccaka daga Mr. Trump dangane da shigar da yayi zuwa ganawar ta ban girma, duk da cewa Trump ya ‘dan yaba masa kan yadda ya sanya ‘yar riga shigen tashi ka fiye naci. Jim kadan da fara tattaunawa kan makasudin taron shugabannin biyu sun hautsune har ta kai su ga caccakar juna kan gazawar kowanne bangare.

Karin bayani: Ukraine ta amince da bukatar cinikin ma'adinai da Amurka 

An dai tashin taron baram-baram ba tare da cimma yarjejeniyar da aka yi niyyar kullawa ba, inda shugaban Ukraine ya fice daga fadar bayan shan wani martanin daga manema labaran Amurka kan shigar kaskancin da yayi zuwa fadar White House da kuma martanin da ya sha daga mataimakin shugaban Amurka JD Vance kan rashin godiya ga tallafin da ya samu na makuden kudade da makamai daga gwamnatin Amurka.

Tun bayan fitar hotuna da bidiyon ganawar shugabannin biyu daga kafafen yada labarai har ma da shafukan sada zumunta. Shugabannin kasashen Turai sun jaddada goyon baya ga Ukraine tare da yin jinjina ga shugaba Volodimyr Zelenskyy kan yadda ya tsaya kai da fata wajen caccakar Amurka da kuma manufofinta na daukar bangare a yakin Rasha da Ukraine.

Karin bayani: Donald Trump ya tsaurara kalamai a kan Zelensky 

Ministar Harkokin Wajen Jamus mai barin gado Annalena Bearbock ta ce Kasashen Turai na tare da Ukraine kuma ba ita ka dai ba ce a wannan yaki. Kazalika shugabannin EU za su gudanar da taro a gobe Lahadi domin sake tattaunawa kan yakin Ukraine.

Shi ko Firaministan Hungary da ke da alaka ta kur-da-kut da Rasha, Viktor Orban,  jinjina ya yi ga shugaban Amurka Donald Trump kan yadda ya yiwa Zelensky wankin babban bargo.

 


News Source:   DW (dw.com)