MDD za ta taimaka wa Afirka saboda yunwa

MDD za ta taimaka wa Afirka saboda yunwa
MDD ta ce zata baa tallafin dala  miliyan 100 ga kasashen Afirka shida hade da Kasar Yemen,domin taimaka musu wajen yaki da matsalar yunwa da ke da nasaba da rugujewar kasuwar abinci sakamakon yakin Ukraine.

Daga cikin wadannan kudade miliyan 14 za su je Somalia, yayin da Habasha za ta samu miliyan 12, Kenya miliyan 4. Sudan miliyan 20. Sudan ta Kudu miliyan 15. Sai Najeriya ita ma  miliyan15. kana Yemen miliyan 20. Kungiyoyin agaji na Majalisar Dinkin Duniya ne sune za su  yi amfani da kudaden wajen sayen abinci da sauran kayayyakin da ake bukata cikin gaggawa domin rarrabawa jama'a. Ukraine da Rasha suna daga cikin manyan kasashe masu samar da hatsi ga ƙasashe masu tasowa da yawa. Sai dai tun farkon yakin kasuwanci ya dakata abin da ya sa farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi a bisa kasuwannin duniya.

 


News Source:   DW (dw.com)