Majalisar Dinkin Duniya, ta yi Allah wadai da abin da ta kira amfani da karfi fiye da kima da hukumomi ke yi a iyakar Spaniya da Moroko, tare da nuna bukatar cikakken bincike a kan kisan wasu bakin haure su 23 a makon jiya.
Kimanin wasu bakar fata mutum dubu biyu ne suka yi kokarin ketare iyakar Morokon da nufin shiga Spaniya, abin da ya haddasa husuma a ranar Juma'ar da ta gabata.
Satatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ta bakin kakakinsa Stephane Dujarric, ya ce mutanen da ake ci musu zarafin a wajen, na da hakkin da dole ne a kiyaye musu.
Mr. Guterres ya kuma tabbatar da cewa ya bi duk wani abu da ya faru a lokacin, saboda haka ne yake kiran da a bi musu hakkinsu.