Tawagar ta UNIFIL mai akalla sojoji dubu 10 a kudancin kasar ta zargi sojojin IDF da kai mata hare-hare tun bayan gargadinsu na su fice daga yankin kudancin Lebanon da suka yi.
Tuni ministocin tsaron kasashen Italiya da Indonesiya da ke da mafi yawan sojiji a tawagar, suka kira jakadojin Isra'ila da ke kasashensu domin bayar da ba'asi a kan harin da ya jikkata dakarunsu.
Wannan harin dai shi ne na baya-bayan nan da ya rutsa da maboyar karkashin kasa da dakarun na Majalisar Dinkin Duniya ke samun mafaka.
Karin Bayani:Yara na kwana a kan titunan Beirut sakamakon rikici