MDD ta yi tir da harin Isra'ila a Gaza da ya rutsa da jami'anta

Jawabin na Blinken da ke zuwa kwana guda bayan wani mumunan harin sojojin Isra'ila a wata makaranta da yaki ya raba Falasdinawa da matsugunnansu ke neman mafaka, wanda ya hallaka mutane 14 ciki har da jami'an Majalisar Dinkin Duniya 6.

Shi ma a nashi bangaren babban sakatare na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna rashin amincewarsa a kan kisan da ma yadda harin da dakarun Isra'ila ke yi na kan mai uwa da wabi a Gaza ke ci gaba da salwantar da rayukan fararen hula, daga ciki harda ma'aikatan agaji da na jami'an MDD da dama tun bayan barkewar yakin a watan Oktoban bara.

Mai magana da yawun Guterres ya ce za a gudanar da bincike mai zaman kansa, tuni kasar Turkiyya ita ma ta ce za ta gudanar da nata binciken.

Ma'aikatar lafiyar Isra'ila ta ce ya zuwa yanzu sama da fararen hula a Gaza 41,000 ne suka rasa rayukansu, mafi akasarinsu mata da kananan yara.

 

Karin Bayani: Ana zargi Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Gaza  


News Source:   DW (dw.com)