MDD ta bukaci Rwanda ta janye dakarunta a Kwango

Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bukaci Rwanda ta janye sojojinta daga gabashin Dimokuradiyyar Kwango, yankin da fada ke kazancewa tsakanin 'yan tawayen M23 da sojin Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango.

Tashin hankalin na tukarar birnin Goma da ya kasance muhimmi ga bangarorin da ke fafatawa da juna saboda albarkatun kasa da ke shimfide a karkashinsa.

Gabashin Jamhuriyar Demokaradiyya Kwango cikin halin yaki

Fadan da ya kaure a baya-bayan nan ya janyo mutuwar dakarun wanzar da zaman lafiya fiye da gomakuma hakan ya tilasta wa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya shirya ganawar gaggagwa da dukkan bangarorin biyu.

Rwanda da Kwango sun janye ma'aikatansu na diflomasiyya daga kasashen juna, sannan Kwangon na zargin Kigali da mara wa 'yan tawayen na M23 baya a gabashin kasar.

Dama an tsara cewa a ranar Litinin ne za a yi ganawar da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya, sai dai lalacewar al'amura ya tilasta yin zaman a ranar Lahadi.

Yadda jama'a ke tserewa rikicin da ya barke tsakanin M23 da sojojin Kwango Yadda jama'a ke tserewa rikicin da ya barke tsakanin M23 da sojojin Kwango Hoto: Jospin Mwisha/AFP/Getty Images

Kwango: M23 ta karbe iko da mahakar ma'adinai ta Rubaya

A daya bangaren, Faransa da Burtaniya sun matsa wa Rwanda lamba kan hannun da ake zargin take da shi a yakin da ke faruwa a kusa da garin Goma na gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango.

Kasashen biyu sun yi kiran ne ranar Lahadi a jawabansu na taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da aka gudanar kan rikicin.

Majalisar Dinkin Duniya da kuma wasu kasashen sun zargi Rwanda da bai wa 'yan tawayen M23 goyon baya, ko da ya ke Kigali ta sha musanta zargin.

Mutane 12 sun mutu a wasu sabbin hare-haren ADF a Kwango

Jakadan Faransa a zauren Majalisar Dinkin Duniya ya nemi Rwanda da ta janye sojojinta daga yankunan Jamhuriyar Dimukradiyyar Kwango, a yayin da shi kuma na Burtaniya ya bukaci a kawo karshen kisan da ake yi wa dakarun wanzar da zaman lafiya.

Burtaniya ta daura laifin kisan ne kan mayakan na M23 wadanda ta yi zargin suna samun goyon bayan Rwanda, duk da cewa kasar ta rika musanta zargin.


News Source:   DW (dw.com)