MDD na son a yi binciken kashe-kashe a Sudan

MDD na son a yi binciken kashe-kashe a Sudan
Bayan kashe-kashen fararen hula da ake zargin jami'an tsaro da aikatawa sakamakon zanga-zangar adawa da gwamnati, Majalisar Dinkin Duniya ta ce a binciki lamarin.

Majalisar Dinkin Duniya, ta yi kira ga hukumomin kasar Sudan da su kaddamar da bincike mai zaman kansa, bayan kisan da jami'an tsaron kasar suka aikata a kan masu zanga-zangar neman kawo karshen mulkin soja a kasar.

Cikin wata sanarwar da shugabar hukumar kare hakkin bil Adama ta Majalisar, Michelle Bachelet ta fitar musamman kan kisan 'yan Sudan din tara a jiya Alhamis, jami'ar ta nuna damuwa kan abin da 'yan sanda suka yi duk da bayanan da suka yi na cewar ba za su amfani da harsasan gaske ba a kan fararen hula.

Mutum 113 ne dai jami'an suka mutu a Sudan, tun bayan karbe iko da sojoji suka yi a watan Oktobar bara, kuma ya zuwa yanzu babu wani da aka dora wa alhakin kisan fararen hulan.


News Source:   DW (dw.com)