MDD: Mutum miliyan 100 ne ke gudun hijira

MDD: Mutum miliyan 100 ne ke gudun hijira
Rikicin Ukraine da kwace ikon da Taliban ta yi a Afghanistan na cikin manyan dalilan da suka kara girman alkaluman 'yan gudun hijira a cewar Majalisar Dinkin Duniya.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta sanar a wannan Alhamis cewa mutane miliyan 100 ne suka kaurace wa gidajensu, suka zama 'yan gudun hijira a shekarar da ta gabata. Wannan shi ne adadi mafi girma da duniya ta taba samu tun bayan yakin duniya na biyu. 

Majalisar ta ce mutane a yankin Sahel na Afirka na kaurace wa gidajensu a sakamakon rashin tsaro da tsadar rayuwa da kuma matsalar sauyin yanayi.

Babban kwamishinan kula da harkokin 'yan gudun hijira na majalisar Filippo Grandi ya ce alkaluman 'yan hijira za su ci gaba da hau-hauwa madamar hukumomi ba su dauki matakin dakatar da tashin hankalin da ke kunno kai a kasashensu ba.


News Source:   DW (dw.com)