Hasashen da Ma'aikatar Tattalin Arziki da Zamantakewa ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi, ya ce yawan al'ummar duniya na karuwa a cikin sauri tun a shekara ta 1950. Ana hasashen samun yawan bil adama biliyan 8 da miliyan 500 a shekarar 2030 sannan adadin zai karu zuwa biliyan 9 da miliyan 700 a shekarar 2050.
Rahoton ya ce yayin da ake samun raguwar haihuwa a kasashe masu tasowa da dama, fiye da rabin hasashen karuwar al'ummar duniya a cikin shekaru masu zuwa zai ta'allaka ne a kasashe takwas, Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Masar da Habasha da Indiya da Najeriya da Pakistan da Philippines da kuma Tanzaniya.