Mayakan M23 na kara kutsa kai yankunan gabashin Kwango

Mayakan na M23 dake samun goyon bayan dakarun Ruwanda a cewar rahotanni tazarar da ke tsakaninsu da garin na Bukavu bai wuce kilomita 60 ba.

Kazalika mayakan na kuma kara nausawa ta babban filin sauka da tashin jiragen sama da ke yankin, a cewar jami'in wanzar da zaman lafiya na MDD Jean-Pierre Lacroix.

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da fara kwashe ma'aikatanta daga wannan yanki dake da dubbunin fararen hula.

Halin da aka shiga DRC musamman ma babban birnin Goma shi ne mafi muni tun a shekarar 2012, kuma rikicin da ya samo asali sama da  shekara talatin da suka gabata tun bayan yakin kare dangin Rwanda.

Karin Bayani: Ana taro kan rikicin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango  


News Source:   DW (dw.com)