Mayakan al-Shabaab sun kashe sojojin Somaliya 13 bayan tashin nakiyoyi a cikin mota a sansanoni guda uku, gwamnati ta yi ikirarin murkushe tasirin hari a wurare guda biyu tare da halaka maya 130.
Sai dai kungiyar ta sanar da kwace makaman sojoji da dama tare da kashe wasu jami'an tsaro 100, babu dai tabbaci kan ikirarin bangarori guda biyu kan sabon harin.
Mayakan al-Shabaab masu kishin Islama na ci gaba da nuna wa gwamnati adawa da tsinin bindiga tsawon shekaru a Somaliya da sauran aksashe makwabta kamar Kenya da Uganda. 'Yan siyasa da 'yan jaridu na cikin mayan wadan da kungiyar ke farauta.