Mayaka sun kashe sojojin Burkina Faso

Mayaka sun kashe sojojin Burkina Faso
Rahotanni daga Ougadugou babban birnin kasar Burkina Faso na cewa akalla dakarun gwamnati bakwai sun mutu, bayan wasu tagwayen harin mayakan jihadi a barikin soji a gabashin kasar.

Rundunar sojojin kasar ta ce hari na biyu ya halaka farar hula daya tare da jikkata wasu da dama da ke cikin motar fasinja.

Harin ya faru ne bayan harin da ya kashe kusan  mutane 40 a ranar Asabar, yawanci fararen hula ne masu aikin sa kai tare da sojoji. Burkina Faso dai ta sha fama da hare-haren masu jihadi tun shekara ta 2015, tare da yunkurin da ke da alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS.

Sama da mutane 2,000 ne aka kashe yayin da miliyan 1.8 suka rasa muhallansu. Sabon shugaban kasar, Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, ya ce ya mayar da matsalar tsaro a matsayin fifiko.


News Source:   DW (dw.com)