Matasa za su kwato mulkin Siriya in ji Iran

 A yayin wani tarin addini da ya jagoranta a wannan Lahadi a birnin Tehran, Khamenei, ya ce matasan Siriya ba za su nade hannayensu su zura wa abin da ke faruwa a kasarsu ido ba, domin hakan shi ne zai ceto makomarsu a nan gaba. 

Faduwar gwamnatin Assad dai ta gigita kasar Iran wacce ta dauke shi a matsayin amini na kut-da-kut a Gabas ta Tsakiya. A karkashin mulkin Assad, Siriyan, ta zama wata hanya da Iran ke bi wajen isar da makamai ga kungiyar Hezbollah a Lebanon, lamarin da ya samar da fahimtar juna a tsakanin Assad da mahukuntan Iran, wadanda suka rika tallafa masa da kudade da ma makamai a yakin basasar da Siriyan ta kwashe shekaru tana cikin sa.

Tuni dai hukumomi a Tehran suka ayyana kungiyar  Hayat Tahrir al-Sham wadda ta kifar da gwamnatin Assad a matsayin ta 'yan ta'adda.

 


News Source:   DW (dw.com)