Matakin Amurka ya shafi ceto a Gaza

Matakin dakatar da samar da kudaden tallafi da Shugaba Donald Trump na Amurka ya dauka, ya haddasa wa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO gibin dala miliyan 46 da ta tsara amfani da su wajen ba da kaurar da wadanda suka yi matukar jikkata a Zirin Gaza.

Haka nan ma hukumar ta WHO ta ce daga ciki ne ta tsara sakegina wasu asibitocin da yaki ya ragargaza a Zirin na Gaza.

A jawabin da ya yi wa manema labarai a Gaza a ranar Talata, mai kula da ayyukan hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya a yankin, Rik Peeperkorn ya ce har yanzu dai ana iya amfani da kudaden da aka samar na tallafi, muddin dai wadanda suka dauki alkawura za su cika.

Cikin watan Janairun da ya gabata ne dai Shugaba Donald Trump ya dakatar da kudaden jinkai, yana mai cewa za a bi diddigin kudaden da ake kashewa ta wannan fuska don ganin dacewar hakan da muradun Amurka.


News Source:   DW (dw.com)