Mataimakiyar shugabar kasar, Sara Duterte ta yi wannan furucin ne a lokacin da take ganawa da manema labarai. Shugabar ta yi ikrarin tuntubar 'yan bindiga da su aika Shugaba Marcos da matarsa da kuma kakakin majalisar wakilan kasar zuwa lahira. Tuni dai rundunar samar da tsaro ta fadar shugaban kasar ta kara tsaurara matakan kare shugaban.
Duterte da ke zama 'ya ga tsohon shugaban kasar, ta dade ta na zargin Shugaba Marcos da rashin iya gudanar da mulki yadda ya kamata. Kana ta yi hannun riga da dukkannin manufofin shugaban, da kuma yakin da mahaifinta ya yi kan ta'amulli da miyagun kwayoyi.
A karkashin dokar hukunta laifuka ta Phillipine, kalamanta ka iya kaita ga zaman kaso da kuma biyan tara. Tun dai a watan Yuni ne ta yi murabus daga majalisar ministocin shugaban yayin da take ci gaba da rike mukaminta na mataimakiyar shi.