Mataimakiyar firaminista kana ministar kudin Kanada ta ajiye aiki

Mataimakiyar Firaministar Kanada kana ministar kudi, Chrystia Freeland ta yi murabus daga bakin aiki kuma tana cikin manyan ministocin gwamnatin Firaminista Justin Trudeau. Wannan matakin ya janyo tambayoyi game da matsayin firaministan.

Karin Bayani: Justin Trudeau zai yi wa'adi na uku

Tuni masu adawa na bangaren masu ra'ayin mazan jiya suka nuna irin radanin da gwamnatin kasar ta Kanada ta shiga, na samun sabani tsakanin mambobin jam'iyya mai mulki.

 


News Source:   DW (dw.com)