Tun da fari, majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar amincewa da tsige Mr. Gachagua sakamakon zarginsa da ruruta rikicin kabilanci da wadaka da dukiyar al'umma har ma da sukar manufofin gwamnatin Nairobi. Matakin kotunan kasar ya haifar da tsaiko wajen gaggauta tsigi mataimakin shugaban kasar ta Kenya.
An dai samu rarrabuwar kawuna tsakanin alkalan kotunan kasar da wata kotun Nairobi ta bada shawarar kafa kwamitin alkalai da zasu yanke hukuncin karshe kan matakin 'yan majalisar.
karin bayani: Tsige mataimakin shugaban kasar Kenya
Rigathi Gachagua ya marawa shugaba William Ruto baya a zaben 2022, wanda ya taimaka matuka wajen samun kuri'un al'ummar lardin tsakiyar Kenya da ke da cunkoson jama'a. To amma a watannin da suka gabata dangantaka ta yi tsami tsakanin shugaban kasar ta Kenya William Ruto da Mataimakinsa Mr. Gachagua.