Mata sun taka rawa a zaben Kenya

Mata sun taka rawa a zaben Kenya
A karo na farko mata sun lashe kujeru masu yawa a zaben Kenya da aka kammala.

Zaben kasar Kenya da aka kammala ya nuna a karon farko mata sun lashe mukamai fiye da kowane lokaci, inda suka samu kejerun mukamun gwamnoni guda bakwai daga cikin 47, da 'yan majalisar dattawa uku gami da 'yan majalisar dokoki guda 26.

A bayan galibi mata suna zuwa majalisar dokoki karkashin kujeru 47, daga kowani yanki na kasar da aka ware wa mata.

Kasar ta Kenya da ke yankin gabashin Afirka ta shafe shekaru tana daukan matakan ganin mata sun kara shiga cikin lamuran harkokin tafiyar da madafun iko.

Mataimakin shugaban kasar Willaim Ruto ya lashe zaben na shugaban kasar Kenya, amma akwai yuwuwar madugun 'yan adawa Raila Odinga zai kalubalanci zaben.

 


News Source:   DW (dw.com)