Mata a Indiya na zanga-zanga kan halaka wata likita

Dubban likitoci mata ne suka fantsama kan tituna a fadin kasar Indiya wajen gudanar da zanga-zanga, don nuna fushinsu kan kisan gillar da aka yiwa wata matashiyar likita a wani asibiti da ke gabashin kasar a jihar Arewacin Bengal.

Karin bayani: Zanga-zangar dokar zama dan kasa a Indiya

An dai samu gawar matashiyar likitar 'yan shekaru 31 a kwalejin asibitin RG Kar da ke Kolkata. Binciken kwakkwafin da aka yi wa gawar an gano munanan raunuka a jikinta da ke alamta cewa an ci zarafinta kafin daga bisani a halaka ta.

Karin bayani: Masu zanga zanga sun mutu a Indiya 

Firaiministan Indiya Narendra Modi, ya nuna takaicinsa kan yadda ake cin zarafin mata a kasar, a wani jawabi da ya gabatar kan cikar kasar shekaru 78 da samun 'yancin kai, Modi ya ce ya damu matuka kan yadda ake gudanar da mummunar ta'addanci akan iyaye mata.

Tuni dai hukumomin yankin suka cafke wani 'dan sandan sa-kai da ake zargi da hannu a kisan matashiyar likitar. Kungiyar Likitoci ta kasar ta Indiya ta ce kaso 75% bisa dari na ma'aikatan lafiya sun taba fuskantar cin zarafi a tarihin aikinsu.

 


News Source:   DW (dw.com)