Bayaga alkaluman na MDD it ma ministar harkokin mata a kasar Jamus ta soki yadda ake samun cin zarafin mata a kasar ta Jamus, Lisa Paus, ta bukaci da majalisar dokokin Jamus ta gaggauta amincewa da dokar hana cin zarafin mata. Ministar na magana ne albarkacin ranar yau ta yaki da cin zarafin mata a duniya. A wani abu mai matukar tada hankali ministar tace a ko wace rana mata 400 ke fiskantar cin zarafi na cikin gida a fadin kasar ta Jamus. Ta kuma kara da cewa bincike ya nuna ko wace rana ana kashe mace daya a kasar Jamus, kuma galibin kisan na faruwa ne bisa rikici tsakanin iyali. An dai yi bukukuwa dama jirin gwano a biranen kasar Jamus da dama a wannan Litinin, don nuna adawa da cin zarafin mata. Shi ma da yake jawabi kan ranar yaki da cin zarafin mata, shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz , ya bukaci da a samar da dokoki masu tsauri don yaki da cin zarafin mata a Tarayyar Jamus wanda ke matukar tada hankali. MDD a rahotonta ta ce mata da 'yan mata 51,100 aka hallaka a fadin duniya, kuma duk wannan alkaluma ne da matan da 'yan uwansu suka hallaka, bawai wadanda ke mutuwa kan titi ba.
News Source: DW (dw.com)