Masu zanga-zanga sun mutu a Sudan

Masu zanga-zanga sun mutu a Sudan
Masu zanga-zanga tara sun gamu da ajalinsu sakamakon aranagamar da ta barke tsakaninsu da jami'an tsaro a wasu sassan Sudan ciki har da babban birnin kasar Khartum.

Dubun-dubatar 'yan kasar Sudan sun fito yin tattaki a wannan Alhamis a cigaba da nuna adawa da gwamnatin mulkin soja karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhane, sai dai daga bisani zanga-zangar ta rikide inda ta koma batakashi tsakanin jami'an tsaro da masu rajin kare dimukuradiyya.

Masu fada a ji daga sassan duniya suka fara sukan lamirin amfani da karfin tuwo wajen tarwatsa masu bore a Sudan, tare da kira ga bangarorin da ba sa jituwa da su saka wa zukatansu ruwan sanyi.

Boren kin jinin gwamnatin mulkin soja ya karade kasar Sudan ne tun bayan da Janar Abdel Fattah al-Burhane ya karbe iko da tsinin bindiga daga wata gwamnatin farar hula ta wucin gadi watanni takwas da suka gabata.


News Source:   DW (dw.com)