Kungiyoyin sun ce tun daga lokacin da aka gudanar da zanga-zangar kin jinin gwamnati a watan Yunin 2024, akalla an sace mutane 82, yayinda wasu mutanen 29 suka yi layar zana ko sama ko kasa.
Karin bayani: Amnesty na son a yi bincike kan murkushe boren matasa a Kenya
Kungiyoyin kare hakkin 'dan adam da dama ciki har da Amnesty International da Human Rights Watch sun zargi 'yan sanda da sauran jami'an tsaro wajen yin garkuwa da mutanen, zargin da 'yan sandan Kenyan ke ci gaba da musantawa. Ko a baya bayannan mutane uku da suka yi kaurin suna wajen caccakar gwamnatin Ruto sun yi batan dabo da suka hadar da Peter Muteti da Billy Mwangi da kuma Bernard Kavuli.
Karin bayani: Matasan Kenya da kafar sada zumunta
Hukumomin kasar ta Kenya sun jinkinta gudanar da bincike kan dauki dai-dai da ake yi wa masu sukar manufofin gwamnatin Shugaba William Ruto a shafukan sada zumunta.