Masu bore sun afka wa majalisar Iraki

Masu bore sun afka wa majalisar Iraki
'Yan sanda sun jefa borkonon tsohuwa amma masu boren suka fi karfin su, suka afka wa ginin da ake kira ''Green Zone'' mai matukar tsaro da ke kunshe da ma'aikatun gwamnati da ofisoshin jakadancin kasashen ketare.

Daruruwan magoya bayan fitaccen malamin Islama a Iraki Moqtada Sadr sun kutse kai zuwa ginin Majalisar Dokokin Kasar domin yin zanga-zangar adawa da zabar wani dan siyasa da Iran ke goya wa baya a cikin wadanda ake sa ran 'yan majalisar za su zaba ya zama firaminista. 


Duk da cewa masu bore ba su riski 'yan majalisa a ginin ba, amma firaministan Iraki Mustafa al-Kadhemi  ya umurce su da su yi gaggawar ficewa daga ginin, yana mai barazanar daukar tsattsauran mataki a kan duk wanda ya yi kokarin lalata kayan gwamnati ko kuma tayar da zaune tsaye. 


News Source:   DW (dw.com)