Masar ta kara bai wa kasar Somaliya manyan makaman yaki.

Makaman da kasar ta Masar ta tura zuwa kasar ta Somaliya sun hada da manyan makaman soja masu cin dogon zango da makaman garkuwa. Tun farko wannan shekara ake kara samun karfafa dangantaka tsakanin kasashen Masar da Somaliya, inda duk kasashen suke da sabani da kasar Habasha. Ita dai Somaliya ta harzika saboda yadda Habasha ta kulla yarjejeniya da yankin Somaliland da ya balle daga kasar. Sannan ita kuma Masar ta fusata saboda yadda Habasha ta gina madatsar ruwa a kogin Nilo.

 


News Source:   DW (dw.com)