Masar ta ce goyon bayan matakin Trump a kan Gaza barazana ne ga yarjejeniya

Masar da ta jima tana zama mai shiga tsakanin a yakin na Gaza, ta ce kalaman wasu jami'an gwamnatin Isra'ila ba zai haifar da komai ba face mayar da hannun agogo baya a yakin.

Har wa yau, Masar din ta ce shirin Trump na fitar da Falasdinawa daga Gaza ya keta dokokin kasa da kasa, sannan yin hakan take hakkin al'ummar Falasdinawa ne.

Shi ma dai babban jami'in kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya Volker Turk ya ce "Duk wani yunkuri na tilastawa mutane shiga ko korar mutanen daga yankunansu da aka mamaye haramtace ne."

Karin Bayani: Gaza: Trump ya bukaci Masar da Jordan su karbi Falasdinawa


News Source:   DW (dw.com)