Martanin kasashen duniya kan kisan al-Zawahiri

Martanin kasashen duniya kan kisan al-Zawahiri
Kasar Saudiyya na daga cikin sahun farko na kasashen da suka yi gaggawar martani a kan kisan shugaban na al-Qaeda, inda ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce ta yi maraba da matakin da Amurka ta suka dauka.

 

Gwamnatin Biden ta yi ikirarin halaka Shugaban kungiyar Al-Qaida Ayman al-Zawahiri a wani harin jirgin yaki mara matuki a Afganistan, marigayi al-Zawahiri mai shekaru 71 a duniya, shi ne magajin Osama bin Laden tun 2011.

Sanarwar da mahukuntan Riyadh suka fitar ta ce Zawahiri na cikin jagororin 'yan ta'adda da suka kitsa munanan hare-hare ba a Amurka kadai ba har ma da kasar Saudiyya. Ita kuwa kasar Ostireliya cewa ta yi kisan na kasurgumin dan ta'addar na duniya zai taimaka wurin rage radadin kuncin da hare-haren Zawahiri suka jefa wasu iyalai a duniya, kamar yadda firaminista  Anthony Albanese ya baiyana.

Halaka  Ayman Zawahri  na cikin manyan kudurorin da tsofaffin shugabannin Amurka irinsu  George W. Bush da Barrack Obama da kuma Donald Trump  suka so aiwatarwa amma abin ya faskara. To sai dai Shugaba mai ci Joe Biden ya ce nasarar da aka samu yanzu ta biyo bayan ingantattun bayanan sirrin da aka yi aiki da su ne. Ya ce tun a farkon shekarar nan suka samu labarin cewa Zawahri ya isa birnin Kabul domin ya gana da iyalansa. Daga nan suka rika bin sawunsa har suka halaka shi ta hanyar hari da jirgi maras matuki a ranar Litinin da daddare.

USA US-Präsident Joe Biden äußert sich zur Tötung des Al-Qaida-Führers Ayman al-Zawahiri

A yanzu dai Amurka da kawayenta na kallon kisan babban dan ta'addar na al-Qaeda a matsayin nasarar yaki da mayaka masu ikirarin jihadi a duniya kamar yadda shugaban Amirka Joe Biden ya nunar inda yake cewa:-

"Yanzu an yi adalci kuma wannan shugaban 'yan ta'adda ba ya raye. Mutane a duk faɗin duniya ba sa bukatar su ji tsoron mugun mai kisa. Amirka na ci gaba da nuna aniyarta da karfinta na kare kasarta daga mugun iri. Muna sake nanata cewa, komin daren dadewa duk inda kuka buya, idan kuna barazana ga mutanenmu, Amirka za ta gano ku."

Manyan jami'ai sun ce ficewar Amirka daga Afganistan a 2021 ya bai wa al-Qaeda damar kara samun karfi a Afganistan, ba tare da wani koma baya ba daga sabuwar gwamnatin Taliban. Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya ruwaito wani jami'in leken asirin Amirka na cewa, gidan da al-Zawari yake a yayin harin mallakin babban mai taimaka wa babban shugaban Taliban Sirajuddin Haqqani ne.

Da alama wannan sabon harin zai dagula dangantakar da ke tsakanin Washington da Taliban.

Me jami'an Afghanistan suka ce?

Da farko ma'aikatar harkokin cikin gida ta Afghanistan ta musanta rahotannin wani hari da jiragen yaki maras matuki suka kai a birnin Kabul. Sai dai kakakin kungiyar Taliban Zabihullah Mujahid ya fada cewa jiragen yakin Amirka marasa matuka ne suka kai wani hari ta sama a wani gida da ke yankin Sherpur na babban birnin kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Taliban ta yi Allah-wadai da harin da Amurka ta kai, tana mai cewa ya kasance "karara keta dokokin kasa da kasa ne da kuma yarjejeniyar Doha.

Wanene Ayman al-Zawahiri?

Al Kaida Anführer Aiman az Zawahiri

An bayyana likitan dan kasar Masar a matsayin daya daga cikin wadanda suka kitsa harin da aka kai Amirka a ranar 11 ga watan Satumban 2001 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 3,000. An haifi jagoran na al-Qaida ne a shekarar 1951. Ya fito daga tsatson wani fitattun iyalai masu daraja a Alkahira. Tun yana matashi, ya shiga haramtacciyar kungiyar 'yan uwa Musulmi. Yana cikin ɗaruruwan da aka kama aka kuma aka tuhume shi da hannu a kisan shugaban kasar Masar Anwar Sadat a shekara ta 1981.

Duk da cewa an wanke shi daga tuhumar, ya shafe shekaru uku a gidan yari na Masar bisa zargin mallakar makamai - al'amarin da aka ce yana da kari. Ya tafi Afghanistan bayan an sake shi, inda ya hadu da Osama bin Laden kuma ya shiga yakin da aka yi da sojojin Soviet. An yi imanin Al-Zawahiri, ya kulla alaka mai karfi da bin Laden a karshen shekarun 1980, lokacin da ya yi jinyarsa a cikin kogo a Afghanistan, a lokacin da Tarayyar Soviet ta kai masa hari. Ya zama na biyu a jerin shugabanin al-Qaeda a 1998. Tun bayan kisan bin Laden da sojojin Amirka suka yi a 2011, al-Zawahiri ya kasance a cikin jerin wadanda hukumar leken asiri ta Amirka FBI ke nema ruwa a jallo, inda suka ware kudi dala miliyan 25 a mastayin tukwici ga duk wanda ya bayar da bayanan inda yake.


News Source:   DW (dw.com)