Maroko ta ce ta tarwatsa yunkurin kai hari a Sahel

Hukumomin kasar Maroko sun kama gomman mutane a baya-bayan nan, da suka yi zargin na shirye-shiryen kai hare-haren ta'addanci a madadin kungiyar IS a cikin kasashen Sahel.

Wannan kamen a cewar hukumomin na Maroko, ya nuna kokarin da kungiyar IS ke yi na fadada ayyukanta a yankin kasashen Afirka bakar fata.

Amma fa gwamnatin ta Maroko ba ta bayar da cikakkun bayanan wadanda ta ce ta kama tsare da sarewa ba, duk da cewar ta sako wasu hotunan da ta ce na wadanda take zargin ne musamman na bidiyo.

Hotunan dai sun nuno har da jerin muggan makaman da 'yansanda suka same su da su tare da tutar kungiyar  ta IS gami da wasu makudan daloli na Amurka.


News Source:   DW (dw.com)