Manyan ministocin Birtaniya sun yi murabus

Manyan ministocin Birtaniya sun yi murabus
Ministocin kudi da na lafiya a Birtaniya sun sanar da yin murabus daga aiki, wani abu da ake ganin koma baya ne ga Firaminista Boris Johnson da ke fama da zarge-zarge.

Ministan kudi Rishi Sunak da na lafiya Sajid Javid duk sun yi murabus din ne a ranar Talata, matakin kuma da ya jawo matsin lamba ga Firaminista Boris Johnson.

Tun da fari dai Firaministan na Birtaniya ya nemi ahuwa a kan wani abin kunya mai nasaba da lalata wanda ya shafi daya daga cikin tsoffin manyan jami'an nasa.

Shi dai Mr. Boris Johnson na fsukantar zarge-zarge da yawan kalamai masu cin karo da juna.

Musamman Firaminista Boris Johnson, ya nemi gafarar 'yan kasar Birtaniya saboda abin da ya bayyana da rashin dacewar tsohon mai tsawatarwa a majlisar dokokin kasar Chris Pincher, wanda aka zarga da aikata lafin da ya danganci badala.


News Source:   DW (dw.com)