Mambobi 64 aka rantsar a majalisar Iraki

Mambobi 64 aka rantsar a majalisar Iraki
Majalisar dokokin Iraki ta rantsar da sabbin mambobin da suka maye gurbin wadanda suka janye bisa umarnin Moqtadar al-Sadr a makon da ya gabata.

A wannan Alhamis majalisar dokokin Iraki ta rantsar da sabbin mambobin da suka kai sittin da hudu, don maye gurbin wadanda suka janye bisa umarnin jagoran 'yan Shi'a Moqtadar al-Sadr a makon da ya gabata.

Kawancen jam'iyun masu tsatsauran ra'ayi da ke dasawa da kasar Iraki, na shirin zaben mambobin da za su cike gurbin wadanda suka janye, a kokarin bayar da damar samun adadin mambobin da za su sake zaben sabon firaiminista a kasar.

Ita dai jam'iyyar Sadr ta matashin shehin malamin Shi'a Moqtadar al- Sadr, wanda baya ga maciji da kasar Iran, ita ce ta samu rinjaye a zaben watan Oktoban bara, amma ta kasa kafa gwamnati saboda rashin samun isassun jam'iyyun da za tayi kawance da su.
 


News Source:   DW (dw.com)