Wannan mataki da hukumomin birnin birnin Bamako suka dauka, ya zo ne bayan wani hari mai muni da wata kungiya mai alaka da al-Qaeda ta kai a Malin a ranar Talata, harin kuma da ya haddasa asarar rayukan gomman sojoji.
Kungiyar ta'addan ta JNIM, ta dauki alhakin harin da aka kai a sansanin horar da jami'an soji a Bamakon da ma filin jirgin sama da ke wajen birnin.
Su dai Fulanin da galibin su makiyaya ne da ke rungume tsarin kiwon dabbobi na gargajiya na baje ne a kasashe da dama na yankin yammacin Afirka.
Kuma suna da adadi mai yawa a cikin mayakan tawaye da ke kai hare-hare a tsakiyar kasar Malin.
Gwamnan yankin Bamako Abdoulaye Coulibaly ya ce za a rufe kasuwannin shanun ne da bai ba da lokacin budewa ba, saboda dalilai masu nasaba da tabbatar da doka da oda.