Gwamnatin mulkin sojin Mali ta kaddamar da bincike kan zargin da ake yi wa sojojin kasar na kisan fararen 24, a karon farko kenan da ta kaddamar da bincike irin wannan tun bayan kwatar mulki a shekarar 2020.
Karin bayani:'Yan tawayen Abzinawa na amfani da jiragen yakin Ukraine
A ranar Litinin 17 ga Fabarairu ne sojojin Mali hadin gwiwa da dakarun haya na Wagner suka tare motoci biyu dauke da fasinjojin da suka taso daga Gao domin zuwa Algeria, sannan suka halaka su, kamar yadda kungiyar kare 'yancin Azbinawan kasar ta yi zargi.
Karin bayani:'Yan tawayen Mali sun kashe gomman mayakan Wagner
Sana da shekaru 10 kenan Mali na fama da rikicin kungiyoyin tawaye masu ikirarin jihadi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane a kasar.