A cewar wata sanarwa da ta fitar a birnin Bamako, Mali ta sanar da janye dakarunta daga cikin sojojin karo-karo na kasashen biyar bisa zargin kungiyar da zama 'yar kora ta wasu kasashen ketare.
Matakin gwamnatin Bamako na zuwa ne bayan da aka kai ruwa rana game da batun gudanar da taron kolin shugabannin kasashen G5 Sahel a Mali, sakamakon kujerar naki da wata kasar ta hau bisa hujjar cewa Mali na fuskantar rudanin siyasa a cikin gida, batun da kuma ya harzuka sojojin da ke mulkin kasar.
Tun bayan kifar da gwamnatin farar hula da kuma amincewa da sojin hayar Wagner na Rasha, Mali ta shiga zaman doya da manja da wasu kasashe wanda har ta kai Faransa janye dakarunta da ke yaki da ta'addanci a kasar, baya ga wasu jerin takunkumai daga kungiyar ECOWAS ko CEDEAO.