Mali ta tabbatar da raba gari da Faransa

Mali ta tabbatar da raba gari da Faransa
A hukumance gwamnatin da ke rike da mulki a Mali ta sanar da bukatar janyewar rundunar sojin Faransa daga cikin kasar don mutunta yarjejeniyar da suka cimma a bara.

Masu rike da madafun ikon Mali sun sanar da ficewa daga cikin yarjejeniyar tsaro da suka kulla da Faransa a hukumance da a farko ya kai ga tsugunar da rundunar sojin Faransan a kasar don taimaka mata yakar ta'addanci, matakin da suka ce baya rasa nasaba da yadda rundunar sojin Faransa ta tafka laifuka na cin zarafin jama'a a tsawon lokacin da aka tsugunar da ita a Malin. 

Wannan ba shi bane karon farko da masu rike da ikon Malin ke fadin hakan sai dai a wannan karon an fitar da wannan sanarwar ta kafar talabijin din kasar inda kakakin gwamnati Kanal Abdoulaye Maiga ya nemi kasar da tayi wa Mali mulkin mallaka, kan ta mutunta yarjejeniyar da suka cimma tun a watan Yunin bara cikin gaggawa, wanda zai kawo karshen hadakar rundunonin kasashen biyu a kasar da ke yankin Sahel mai fama da hare-haren 'yan ta'adda.

Kawo yanzu babu martani daga mahukuntan na Paris da ke son ganin an mayar da kasar ta Mali kan tafarkin mulkin dimokradiya tun bayan juyin mulkin sojoji har sau biyu a cikin shekara guda.
 


News Source:   DW (dw.com)