Gwamnatin soja a Mali ta bi sahun takwarorinta na Burkina Faso da Nijar wajen sake sunayen tituna da wasu fitattun wurare a Bamako, inda ta ciccire duk wasu sunayen masu alaka da Faransa.
Matakin ya shafi titin CEDEAO da ke nufin ECOWAS a Faransanci wanda aka maye shi da AES a yanzu.
Kusan dai sunayen tituna 25 ne jami'an, hukumomin na Mali suka sake su ciki har ma da wasu da ke na ma'aikatu a Bamakon da duk ke da alaka da turawan mulkin mallaka.
Cikin shekaru biyun da suka gabata ne dai kasashen Nijar da Burkina Faso sun sake sunayen fitattun wurare na tarihi da ma tituna wadanda ke da nasaba da Faransa.
Karkashin ikon Kanal Assimi Goita, kasar Malin ta dakatar da dadadden kawance da ke tsakaninta da kasashen Turai musamman ma kasar Faransa da ta rene ta, sanna ta koma hulda da Rasha musamman ma ta fuskar soji.