Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Mali kanal Assimi Goita da wasu manyan jami'an diflomasiyar kasar Rasha ne suka kaddamar da bikin saukar jiragen a Mali. Wannan dai ba shi ne karon farko da kasar ta Mali ke samun jirage da ma kayayakin yaki da 'yan ta'adda daga kasar ta Rasha ba.
A jawabin da ya gabatar, ministan tsaron kasar Sadio Camara ya ce wannan bikin na cike da tarihi sakamakon shirin murkushe mayakan 'yan ta'adda a kasar. Ya kuma jinjina wa dangantakar da ke tsakanin Mali da Rasha, wadda ya ce suna fatan ganin dorewar ta.