An sako sojoji mata guda uku daga cikin sojin Côte d'Ivoire 49 da kasar Mali ke tsare da su tun cikin watan Yulin da ya gabata. Hukumomin kasar Togo da shugabansu Faure Gnassingbe ke shiga tsakanin Mali da Côte d'Ivoire a kan tsare sojojin ne suka sanar da haka, inda suka ce tuni wadannan mata suka isa gida Côte d'Ivoire. Ministan harkokin wajen Togo ya ce ana ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Mali domin ganin ta hanzarta sakin sauran sojojin Côte d'Ivoire 46 da har yanzu ke hannunta.
Tun da farko dai an aike da sojojin Côte d'Ivoiren kasar Mali domin su yi aiki a wani kamfanin samar da tsaro mai zaman kansa da ke da alaka da ayyukan Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai isar sojojin Mali, hukumomin Bamako suka kama su da laifin zama sojin haya da ke da niyyar kawo wa harkokin tsaron Mali barazana, lamarin da ya haifar da zaman doya da manja na diflomasiyya a tsakanin kasashen biyu makwabtan juna.