Wata sanarwar da ta fitar a wannan Alhamis, rundunar ta sojan Mali ta ce ta yi nasarar kashe mayakan jihadi hudu a yankin Niono da wasu karin 'yan ta'adda 15 a yankunan Manfouné da Vaneku da kuma Mandiyaku, dukkaninsu da ke yankin tsakiyar kasar.
Sai dai wannan sanarwar ta sojan Mali na zuwa ne a yayin da kwararru daga Majalisar Dinkin Duniya ke shirin aiwatar da bincike game da zargin kisan fararen hula akalla 300, da ake tuhumar dakarun kasar ta Mali da aikatawa a farkon wannan wata bisa zarginsu da zama 'yan ta'adda a yankin Mura da ke tsakiyar kasar.