Jami'an tsaro a kasar Mali na cigaba da tsare wasu sojojin Côte d'Ivoire kimanin 50 da suka kama daga filin jirgi na birnin Bamako bisa tuhumarsu da shiga kasar ba tare da ka'ida ba.
An jibge sojojin a wata makarantar horar da jami'an Genderme da ke wajen Bamako kafin kammala bincike, ko da yake wata majiyar diflomasiyyar Côte d'Ivoire ta ce dakarun wani bangare ne na ma'aikatan kamfanin Jamus SAS da ke lura da harkokin filayen jiragen sama.
Tun a wannan Lahadi aka soma baza labarin kama sojan a shafukan shada zumunta, bisa zargin cewa sun shiga kasar Mali ne da yunkurin kifar da gwamnati, sai dai gwamnatin Côte d'Ivoire ta nace cewa ta sanar da fadar gwamnati ta birnin Bamako da cewa dakarunta na shirin shiga kasar.