Hukumomin kasar Mali sun hana sojojin Jamus takwas ficewa daga kasar da ke Yammacin Afirka. Wannan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan gwamnatin mulkin sojan Malin ta kama sojoji kusan 50 na kasar Côte d'Ivoire wadanda ta ce sun isa kasar ba tare da izini ba.
A ranar Alhamis, gwamnatin Malin ta dakatar da tsarin karba-karba na kewayawa da sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da aka fi sani da MINUSMA na dan wani lokaci.