Mali ta dakatar da kewayen sojojin MINUSMA

Mali ta dakatar da kewayen sojojin MINUSMA
Gwamnatin Mali da sojoji ke jagoranta ta ce za ta dakatar da tsarin karba karba na kewayawa da sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA zuwa kasar na dan wani lokaci.

Ma'aikatar harkokin wajen Mali a birnin Bamako ta ce dakatar da kewayawar sojojin na MINUSMA ya hada har da wadanda aka shirya turawa zuwa kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce dakatarwar za ta cigaba har zuwa lokacin da za ta yi taro domin tsara yadda za a gudanar da kewayen sojojin.

Wannan mataki na zuwa ne yan kwanaki bayan da kasar ta ce ta kama sojoji 49 na kasar Ivory Coast wadanda ta ce sun isa kasar ba tare da izini ba.

Sojojin da ke mulki a Mali wadanda suka yi juyin mulki a watan Augustan 2020 sun sha takun saka da kasashen da ke hulda da Mali bayan sanya musu takunkumi da Allah sakamakon jinkirta zabe don mayar da kasar kan turbar dimukuradiyya da kuma kawancen tsaro da suka kulla da sojojin haya na Rasha.

An kaddamar da rundunar kiyaye zaman lafiyar ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali a 2013 domin taimakawa kasar shawo kan kalubalen mayakan jihadi da suka addabi kasar.

Rundunar na daya daga cikin dakarun kiyaye zaman lafiya mafi girma na Majalisar Dinkin Duniya inda ta ke da sojoji 12,200 da yan sanda 1,700 wadanda kasashe kimanin 50 suka bada karo-karo don aikin kiyaye zaman lafiya a Mali.

 

 


News Source:   DW (dw.com)