A wata sanarwar da ta fitar, fadar mulki ta Bamako ta ce ta kama sojin da suka kudiri aniyar mayar da hannun agogo baya a daren 11 zuwa 12 ga wannan watan, tare da zargin wata kasar waje da hannu kai tsaye wajen kitsa makarkashiyar, sai dai kuma gwamnatin ba ta yi wani karin haske kan kasar da take zargi ba. Tuni dai mahukuntan na birnin Bamako suka kara tsaurara matakan tsaro kan iyakokin fita daga babban birnin da ma daukacin iyakokin kasar baki daya.
Tun bayan juyin mulkin da soji suka yi wa wata gwamnatin farar hula ta rikon kwarya a watan Mayun bara, sabbin mahukuntan na Mali suka fada zaman doya da manya wasu kasashen duniya ciki har da Faransa da ta yi wa kasar mulkin mallaka, lamarin da ya kai ga Faransar janye sojojinta da ke yiki da ta'addanci.