Jamus ta dakatar da aikin wani bangare na dakarun sojinta da ke karkashin Majalisar Dinkin Duniya a Mali har sai abin da hali ya yi. Kakakin ma'aikatar tsaron Jamus ya ce fadar mulki ta birnin Bamako ta yi kememe na hana tashin wani jirgin sojin Jamus da ke daukar askarawanta zuwa fagen daga, wanda haka ya harzuka gwamnatin Berlin.
Daga yanzu Jamus ta dakatar da duk wani aikin leken asirri da dakon kayayakin bukatun yau da kullum na soji, da rundunarta ke yi a karkashin jagorancin Minusma, in ji kakakin ma'aikatar tsaron Jamus a gaban manema labarai.
An jima ana kai ruwa rana tsakanin Mali da sauran manyan kasashen yammacin duniya, tun bayan da sojoji karkashin jagorancin Assim Goita suka hambarar da gwamnatin mulkin farar hula watannin da suka gabata.