Malala Yousafzai na ziyara a mahaifarta

Malala ta bar Pakistan a 2012, bayan mayakan Taliban sun bude mata wuta a lokacin da take kan ganiyarta ta fadakar da yara mata muhimmancin ilmi.

Malala wacce ta samu kyautar zaman lafiya ta Nobel na ziyara a Pakistan da ke makwabtaka da Afghanistan, kasa daya tilo da ta hana mata zuwa makaranta domin neman ilmi a fadin duniya. 

Malala ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa tana cike da murna da farin ciki na sake dawowa gida domin ganawa da mata kan batun ilmi.

karin Bayani:Hunkunci a kan 'yan Taliban waÉ—anda suka nemi kashe Malala Yousafzai  


News Source:   DW (dw.com)