Makomar Ukraine bayan yaki

A cewar shugabannin yayinda ake lalubo hanyar warware yakin Ukraine da ma shata makomar kasar bayan yakin ta da Rasha, to ko da kuwa babu wakilcin Ukraine shugabannin a EU suna iya daukar matakin da suka ga ya dace wa Ukraine. Wannan na zuwa ne ana wata guda gabanin rantsar da shugaban Amirka mai jiran gado Donald Trump, wanda tuni majiyoyi masu karfi suka tabbatar cewa da zaran ya hau kan mulki, to yakin Ukraine ya zo karshe ko ana so ko ba a so. Dama kuwa Trump da mataimakinsa suna matukar adawa da yakin Ukraine tun gabanin su fara yakin neman zabe, kuma da batun na kawo karshen yakin suka yi yakin neman zabe, inda suka ce yakin na lakume biliyoyin kudin Amirkawa da babu dalilin yin hakan. 


News Source:   DW (dw.com)