Majalisar Dinkin Duniya za ta tattauna kan rikicin DRC

Kwamitin kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya zai tattauna kan rikicin da ake fama da shi a gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo a ranar Juma'a.

Gwamnatin Kinshasa ta fada cewa sama da mutum 3,000 aka kashe tare da daidaita fiye da 700,000 tun fara yaki da 'yan tawayen M23 wadanda ake zargin na samun goyon bayan Rwanda.

Sojojin DRC na gumurzu da M23 a Goma - Tshisekedi

Hukumomi sun fada cewa an yi wa mata da dama fyade a wani gidan yari a wannan lokacin da aka kwashe ana fafatawa tsakanin dakarun DRC da kuma 'yan tawayen na M23.

Yankin gabashin Kongo mai arzikin ma'adinan zinare da kobalt da sauransu ya sha fama da tashin hankali na tsawon shekaru inda DRC ke zargin makwabciyarta Rwanda da neman mallake ma'adinan.

M23 ta kwace iko da babban filin jirgin saman Goma

A ranar Alhamis Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutterres ya yi gargadin cewa yakin da ake yi a Kongon ka iya fantsama a yankin gaba daya.


News Source:   DW (dw.com)