Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin duniya, Filippo Grandi ya yi kiran da a taimaka wa al'umomin da sabon rikici ya rutsa da su a Labanan.
Jami'in na Majalaisar Dinkin Duniyar dai ya yi kiran ne a ziyarar da ya kai wa yankunan da ake tsugunar da mutane a Beirut babban birnin kasar ta Labanan .
A cewarsa rikicin da ya kunno kai tsakanin Isra'ila da kungiyar Hezbollah na azaftar da jama'a, yana mai nuna cewa dole ne dokokin agaji na duniya su yi aiki a Labanan din.
Akalla dai akwai kimanin mutane miliyan daya da dubu 200 da suka rasa muhalli cikin makonni biyu da rikicin ya barke.
Sama da dala miliyan 425 ne dai hukumar agajin ta Majalisar Dinkin Duniya ke bukata domin samar da agaji a Labanan din nan da karshen wannan shekara.