Mahmoud Youssouf ya zama sabon Shugaban Kungiyar AU

Shugabannin kasashen Afirka sun zabi Ministan harkokin wajen Djibouti a matsayin sabon shugaban kungiyar kasashen Afirka ta AU a ranar Asabar.

Mahmoud Ali Youssouf ya doke abokan karawarsa kamar Raila Odinga tsohon Firaministan Kenya da Richard Randriamandrato tsohon ministan harkokin wajen kasar Madagascar.

Rikice-rikice za su mamaye taron shugabannin Afirka

An yi zaben ne a yayin babban taron kungiyar kasashen na AU a birnin Addis Ababa na Habasha a gaban wakilan kungiyoyin sa ido da dama.

Kungiyar AU na da mambobi 55 kuma shugabannin gwamnatocin kasashe kan zabi sabon shugaba a babban ofishinta da ke Addis Ababa.

Youssouf wanda zai yi wa'adin shekara hudu, zai maye gurbin Moussa Faki na kasar Chadi wanda ya ke rike da shugabancin kungiyar tun a shekara 2017.

An bude taron koli na kungiyar AU

Wannan sakamakon ya zama tamkar kalubale ga Raila Odinga na Kenya wanda ya rika neman goyon baya a ciki da wajen kasarsa domin darewa kan kujerar ta shugabancin AU.


News Source:   DW (dw.com)