Wani dan kasar Afganistan ya amsa cewa ya afkawa dandazon mutane a birnin Munich na Jamus da mota da gangan, abin da ya raunata mutane 36 ciki har da yaro karami. A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai, maharin mai shekaru 24 a duniya ya fka cikin dandazon mutane da ke jerin gwano a tsakiyar birnin na Munich gabanin zaben 'yan majalisun dokoki na kasa da za a gudanar.
News Source: DW (dw.com)