Rahotanni majiyoyin tsaro a Najeriya, na cewa akalla sojojin kasar 30 sun mutu a wani harin kwantan bauna da ‘yan bindiga su ka yi musu a yankin Shiroro na jihar Neja a farkon mako mai karewa.
Sojojin na cikin jami'an tsaron da aka tura domin neman ma'aikatan hakar ma'adinai da aka sace a ranar Laraba, ciki har da 'yan kasar China hudu.
Babu tabbacin kungiyar da ta kai wannan mumunar hari a kauyen Ajata Aboki da ke jihar Niger a arewa maso yammacin Najeriya, sai dai Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa na twitter a jiya Asabar cewa " ‘yan bindigar ‘yan bakin ciki ne, kuma za su fuakanci hukunci. Mazauna Shiroro za su ga adalci."