Mahara sun kashe mutane 10 a jihar Borno

Mahara sun kashe mutane 10 a jihar Borno
Rahotanni daga Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya sun tabbatar da cewa mayakan da ke ikrarin jihadi sun kashe mutane 10.

Harin ya auku ne a kauyen Goni Kurmi da ke kusa da garin Bama na jihar. Majiyoyi sun ce wadanda suka gamu da ajalin nasu, 9 daga cikin su maza da mace guda na aikin balla karafuna ne daga jikin wata tsohuwar mota a lokacin da mahara da ke da alaka da kungiyar IS suka afka musu.

Wani jami'in sa kai ya ce sun kai gawwawakin garin Bama. Tuni dai aka tura da dakarun soji zuwa yankin, sai dai kawo yanzu babu sanarwa daga bangarensu. 

A baya-bayan nan, masu sana'ar Bola Jari na fuskanta hare-hare daga mahara, saboda zargin da suke musu na kasancewa masu leken asiri da ke yiwa jami'an tsaro aiki.


News Source:   DW (dw.com)